Alban BagbinErnestina Naadu Mills and Alban Bagbin at USAIDSpeaker Alban Bagbin
Alban Sumana Kingsford Bagbin (an haife shi a ranar 24 ga watan Satumba , Shekara ta alif ɗari tara da hamsin da bakwai ( 1957) ɗan siyasan Ghana ne wanda yake shugaban majalisar dokokin Ghana na yanzu.[1][2][3][4][5] Ya kasance Ministan Lafiya a gwamnatin kasar Ghana daga watan Janairu, shekarar 2012[6] har zuwa watan Fabrairu, shekarar 2013 lokacin da Hanny-Sherry Ayittey ta karbi mukamin. Ya taba zama dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Nadowli ta Yamma a yankin Upper West Ghana a majalissar dokoki ta 1,2,3,4,5,6 da 7 a jamhuriya ta 4 ta Ghana.[7] Ya tsaya takarar neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar National Democratic Congress a shekarar 2019 amma daga baya ya sha kashi a hannun tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama.[8] A ranar 7 ga watan Janairu, shekara ta 2021, aka zaɓi Bagbin Kakakin Majalisa ta 8 na Jamhuriyya ta Hudu.[2][9]